Yayin da ke ci gaba da bayyana sakamakon zaɓen gwamnan jihar Edo da aka gudanar ranar Asabar 21 ga watan Satumba, manyan jam’iyyun siyasar jihar biyu na ci gaba da yin kankankan.
Shugaban Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Minna, Farfesa Farouk Adamu Kuta ne babban jami’i tattara sakamakon zaɓen gwamnan jihar.
Babbar Jami’ar INEC ta ƙasa da ke kula da zaɓen, Farefesa Rhoda Gumus ta ce a halin yanzu akwai sakamakon ƙananan hukumomi 14 zuwa 15 a zauren tattara sakamakon.
Kawo yanzu an bayyana sakamakon ƙananan hukumomi 11, yayin da sakamakon ya nuna cewa jam’iyyar PDP mai mulkin jihar ta samu ƙananan hukumomi biyar, inda ta lashe ƙananan hukumomi huɗu daga ciki, inda APC lashe ƙananan hukumomi shida daga ciki.