Tsohon shugaban jam’iyyar APC na Najeriya, Abdullahi Umar Ganduje ya ce akwai butuwa uku da ya sa suka kira taron jiga-jigan APCn Kano a Abuja.
A yau ne jiga-jigan jam’iyyar suka gudanar da wani taro a Abuja.
Tsohon gwamnan na jihar Kano Abdullahi Ganduje ya ce abu na farko da ya sa suka kira taro shi ne taya juna murna kan irin nasarororin da APC ta samu a Kano tun bayan faɗuwa zaɓen gwamnan jihar.
Ganduje ya kuma ce abu ne biyu shi ne domin tsara shrye-shirye da dabarun samun nasarar APC a zaɓe mai zuwa.
”Abu na uku kuma shi ne domin gode wa shugaban ƙasa, Bola Tinubu kan irin ayyukan gwamnatin tarayya da ake yi a jihar kano, da kuma tarin muƙaman da ya bai wa Kano a gwamnatinsa”, in ji Ganduje.







