Home Ketare Yadda al’ummar ƙabilun asali na Amurka ke rayuwa

Yadda al’ummar ƙabilun asali na Amurka ke rayuwa

419
0

Duk da ci gaba irin na ƙasar Amurka, ɗaya daga cikin munanan abubuwan da suka yi mata tabon da ba zai taɓa gogewa ba shi ne halin da aka jefa ƙabilu mazauna ƙasar na asali tun kafin isar mutane daga nahiyar Turai.

A yanzu Turawa da sauran al’umma sun mamaye ƙasar ta Amurka daga kowane ɓangare na duniya, kuma idan har kana son sanin asalin al’umma ko ƙabilun da suka kasance a ƙasar tun kafin zuwan baƙi sai ka je wasu yankuna na gefen ƙasar.

Wannan ne ya sa na kai ziyara wani yanki da ake kira Grand Portage da ke iyaka da ƙasar Canada ta arewacin jihar Minnesota da ke Amurka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here