Bayern Munich ta hakura da tsawaita zaman Alphonso Davies a kungiyar, yayinda Real Madrid ta shiga farautar ɗan wasan mai shekara 23 daga Canada.
(Relevo – in Spanish)
Ɗan wasan baya a Arsenal da Japan, Takehiro Tomiyasu, mai shekara 25, ya ja hankalin ƙungiyar Napoli da Inter Milan.
(Calciomercato – in Italian)
Kocin AC Milan Paulo Fonseca, da ta fafata da abokiyar hamayyarta Inter Milan a ranar Lahadi, ya ce baya wani tunina kan raɗe-raɗin da ake yaɗawa kan makomarsa bayan rashin tabuka abin kirki a farkon kaka.
(Football Italia)
Kocin Liverpool Arne Slot ya ce kungiyar ta warware daga gazawar da ta fuskanta wajen sayen ɗan wasan Sifaniya da ke buga tsakiya Martin Zubimendi ɗan shekara 25 daga Real Sociedad a lokacin bazara. (Mirror)