Home Labarai Duniya Wasu rahotanni sun bayyana cewa Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu na Shirin...

Wasu rahotanni sun bayyana cewa Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu na Shirin maye gurbin mataimakin sa Kashim Shattima da Rabi’u Musa Kwankwaso

25
0

Rahotanni na nuni da cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu na shirin maye gurbin mataimakinsa, Kashim Shettima, da tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma jagoran jam’iyyar NNPP, Rabi’u Musa Kwankwaso, a matsayin ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa a zaɓen 2027.

Wasu majiyoyi masu tushe sun bayyana cewa jagororin siyasar Tinubu na kokarin dawo da Kwankwaso cikin jam’iyyar APC mai mulki, domin ƙarfafa samun nasarar tazarcen shugabancin Tinubu a 2027.

Jaridar Business Day ta rawaito cewa tuni Kwankwaso ya gana da shugaban kasa Bola Tinubu kan wannan batu
Ko da abinda ya faru tsakanin Shugaban Jamiyyar APC Dr Abdullahi Umar Ganduje da magoya bayan mataimakin shugaban kasa Kashin Shettima a wurin taron jamiyyar a jihar Gombe, jaridar tace na da alaka da kokarin dawo da Kwankwaso jamiyyar APC

Duk da cewa Kwankwaso ya kare a mataki na 4 be a zaben shugaban kasar 2023, amma tawagar Tinubu na ganin ƙarfinsa a ƙasa zai taimaka wajen ƙarfafa APC a yankin Arewa maso Yamma.

Wannan sabon shiri na Tinubu ya ƙara ƙaimi ne a daidai lokacin da manyan jiga-jigan adawa irin su Atiku Abubakar na PDP da Peter Obi na Labour Party ke ci gaba da tattaunawa kan kafa sabuwar jam’iyya, wacce ake kira All Democratic Alliance (ADA) domin fuskantar Tinubu a 2027

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here