A cewarsa, muhimman cibiyoyin da ke da alaka da haɓaka makamashi sun kubuta daga harin Amurka, kuma Iran za ta ci gaba da shirinta na kera makaman nukiliya.
Medvedev ya ce gwamnatin Iran ta ƙara ƙarfi, inda ma jama’ar da ba sa goyon bayanta a baya suka fara marawa ƙasar baya.
Haka kuma, ya bayyana cewa ƙasashen duniya da dama sun nuna rashin amincewarsu da matakin da Amurka da Isra’ila suka dauka, inda wasu har suka nuna niyyar bai wa Iran makaman nukiliya.
Medvedev ya zargi shugaban Amurka Donald Trump da jefa ƙasar cikin wani sabon rikici, yana mai cewa ya manta da burinsa na lashe lambar yabo ta zaman lafiya ta Nobel.