Home Labarai Duniya Naira biliyan huɗu sun shigo hannunmu a matsayin tallafi – Zulum

Naira biliyan huɗu sun shigo hannunmu a matsayin tallafi – Zulum

174
0

Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya bayyana cewa ya zuwa ranar Lahadin da ta gabata, gwamnatin jihar ta karɓi kusan naira biliyan huɗu da rabi daga cikin fiye da naira biliyan 13 da aka yi musu alƙawari a matsayin tallafi ga waɗanda ibtila’in ambaliya ya shafa a Maiduguri.

“…naira 4,441,494,902.81 ne suka shigo hannunmu daga cikin alƙawuran N13,195,500,000 da aka yi mana. Za mu ci gaba da sanar da jama’a duk lokacin da aka samu ƙarin shigowar kuɗi” In ji gwamna Zulum.

Farfesa Zulum ya bayyana hakan ne a lokacin da yake kafa kwamitin mutum 35 da zai kula da raba wannan tallafi ga waɗanda al’amarin ya shafa.
Wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar, Bukar Tijjani ya fitar, ya wallafa a shafin X na gwamna Zulum, gwamnan ya ce kwamitin zai ƙunshi wakilai daga hukumomi da dama da suka haɗa da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC da takwararta ta ICPC da kuma hukumar tsaro ta farin kaya wato DSS.

Sauran mambobin kwamitin sun haɗa masu ba wa gwamnan shawara da wakilan hukumar raya yankin arewa maso gabas (NEDC) da ma’aikatar wasanni da ci gaban matasa da ma’aikatar kuɗi da ta mata da kuma hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar (SEMA) da sauransu.

Gwamna Zulum ya buƙaci mambobin kwamitin da su jajirce wajen sauke nauyin da aka ba su da kuma yin gaskiya.
“Za mu tabbatar da cewa an yi amfani da kuɗin ta hanyar da ta dace, za mu tsaya mu ga tallafin ya kai ga mutanen da aka yi domin su,” in ji Zulum.

Ya ce gwamnatin jihar za ta tabbatar da ganin an sake gyara wurare kamar asibitoci da hanyoyi da kuma gadoji.

Mutane da dama dai, musamman masu hannu da shuni suka bayar da tallafin kuɗaɗe da kuma kayan abinci zuwa ga waɗanda ambaliyar Maiduguri ta shafa.

Ya ce sun samu karɓar tallafi da ya kai naira biliyan 4.4 zuwa cikin asusun tallafin jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here