Home Wasanni Man City na son Musiala, Madrid na zawarcin Lukeba

Man City na son Musiala, Madrid na zawarcin Lukeba

146
0

Manchester City na farautar ɗan wasan Jamus Jamal Musiala, mai shekara 21, amma tana fuskantar kalubale daga Real Madrid da itama ke bibbiyar ɗan wasan tsakiyar a Bayern Munich.
(Teamtalk)
Ɗan wasan gaba a Ingila, Dominic Calvert-Lewin ba shi da niyyar tsawaita zamansa da Everton, yayinda Newcastle United ke cigaba da nuna kwaɗayinta kan ɗan wasan mai shekara 27.

(CaughtOffisde)
Kwantiragin mai tsraon baya a Liverpool, Trent Alexander-Arnold na gab da karewa a sabuwar kaka kuma ɗan wasan mai shekara 25 daga Ingila, ya ce lashe kofi ne abin da zai fi bai wa fifiko a lokacin nazarin tsawaita zamansa.

(Liverpool Echo)
Arsenal da Chelsea da Liverpool da Tottenham na farautar ɗan wasan Sporting da Sweden, Viktor Gyokeres, mai shekara 26.

(Teamtalk)
Newcastle ta kasance kungiyar firimiya ta baya-bayanan da ke shiga zawarcin ɗan wasan Amurka amma asalin Italiya, Luca Koleosho, mai shekara 20, da ke jan hankalin Burnley. (HITC)
Kungiyoyin firimiya da na Europa na kokarin ganin sun fito da tsarin da zai ba su damar kammala cinikin ‘yan wasa a sabuwar kaka kafin a soma wasanni.

(Mirror)
Tsohon kocin Brighton da Chelsea, Graham Potter zai iya karban aikin Everton idan aka ba shi dama.(Football Insider)
Real Madrid na bibbiyar ɗan wasan RB Leipzig da Faransa, Castello Lukeba, mai shekara 21. (Marca – in Spanish)
Aston Villa da Fulham da Nottingham Forest na bibbiyar ɗan wasan Galatasaray, mai shekara 24 Baris Alper Yilmaz, yayinda Forest da Brighton da Tottenham ke farautar ɗan wasan nan mai shekara 19 na Turkiyya, Semih Kilicsoy, da ke taka leda a Besiktas. (CaughtOffside), external
Mai sa ido kan ‘yan wasa daga Manchester United da Newcastle da Tottenham na bibbiyar ɗan wasan Ingila, Tyler Dibling, mai shekara 18, daga Southampton. (HITC)

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here