Home Labarai Duniya GIDAN REDIYO DA TALABIJIN NA FORTUNES ZAI TALLAFA WA RUNDUNAR SOJI A...

GIDAN REDIYO DA TALABIJIN NA FORTUNES ZAI TALLAFA WA RUNDUNAR SOJI A KOKARINTA NA SAMAR DA INGATACCEN TSARO

471
0

Shugaban Gidan Radio da Talabijin na Fortunes, Alhaji Ibrahim Magaji Dosara, ne ya bayyana hakan lokacin da ya jagoranci ziyarar aiki ga Babban Kwamandan Rundunar Soji Ta Daya da ke Kaduna, Manjo Janar Lander David Saraso.

 

Dosara yace kafar ta kudiri yin hadin gwiwa da Rundunar Soji Ta Daya da ke Kaduna, domin tallafa wa kokarin kawar da ‘yan ta’adda da fuskantar matsalolin tsaro a kasar nan.

 

Ya kuma bayyana wa kwamandan wasu daga cikin irin shirye-shiryen da suke gabatarwa wadanda suka shafi ayyukan soja, da kuma yunkurin fadakar da jama’a game da harkokin tsaro da hanyoyin magance kalubalen tsaro a kasa.

 

A nasa jawabin, Babban Kwamandan Rundunar Soji Ta Daya, Manjo Janar Lander David Saraso, ya jinjinawa ziyarar da shugabannin Tashar Fortunes din suka kawo, tare da bayyana irin nasarorin da rundunar ta samu karkashin jagorancinsa, musamman wajen dawo da zaman lafiya a manyan hanyoyin Kaduna-Birnin Gwari, Kaduna-Kachia, da Kaduna-Abuja.

 

Haka kuma, Manjo Janar Saraso ya yaba wa kafafen yada labarai bisa yadda suke jajircewa wajen yada rahotannin ayyukan soja a Jihar Kaduna da ma kasa baki daya