Tsohon gwamnan Kano kuma jagoran jam’iyyar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso, ya musanta rahotannin da ke yawo a shafukan sada zumunta da ke cewa ya tura takardar neman shiga wata jam’iyyar siyasa a ƙasar.
Ya bayyana cewa labarin ba gaskiya ba ne, yana mai jaddada cewa ba su nemi shiga wata jam’iyya ba.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake yaɗa jita-jita cewa Kwankwaso da tawagarsa na shirin komawa jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya.
A cikin wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na X, Kwankwaso ya ce: “Mun samu labarin wasu jita-jita a shafukan sada zumunta cewa mun gabatar da takardar niyyar shiga wata jam’iyyar siyasa a ƙasar. Muna so mu fayyace cewa ba mu gabatar da irin wannan bukata ga kowace jam’iyya ba.”
Sanarwar ta kara da cewa irin waɗannan rahotanni na bogi ba su da wata manufa face rikita jama’a da kuma yaɗa ƙarya..
“Jama’a su yi hattara da irin waɗannan labarai na bogi da ake yadawa don daukar hankalin mutane kawai,” in ji Kwankwaso.
Kwankwaso ya kuma shawarci jama’a da su ci gaba da bibiyar sahihan bayanai daga ofishinsa da hanyoyin sadarwa na hukuma







