Home Labarai Duniya Najeriya ta fitar da taken bikin ƴancin kai na shekarar 2025

Najeriya ta fitar da taken bikin ƴancin kai na shekarar 2025

57
0

Gwamnatin Najeriya ta fitar da taken bikin ƴancin kai na shekarar 2025. Taken shi ne “ Nigeria@65: Dole mu haɗa hannu domin ciyar da ƙasa gaba.”

Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da daraktan bayani da hulɗa da Jama’a, Segun Imohiosen, ya fitar a ranar Laraba a Abuja.

Sanarwar ta bayyana cewa taken na nuni da buƙatar haɗin kai da aiki tare da kishin kasa tsakanin hukumomin gwamnati da masu zaman kansu da ƙungiyoyin farar hula, da ‘yan ƙasa baki ɗaya domin tabbatar da zaman lafiya da arziki, da ci gaban kasa.

Gwamnati ta ce zaɓen wannan taken yana nuna juriya da ƙwarin guiwar Najeriya tun samun ‘yanci a shekarar 1960, tare da jaddada muhimmancin karfafa nasarorin da aka samu a baya yayin da ake neman cimma manyan manufofi.

Daga cikin ayyukan da aka tsara gudanarwa don bikin ƴancin kai na Nigeria@65 akwai Sallar Juma’a a ranar 26 ga Satumba da addu’o’i a coci daban-daban a ranar 28 ga Satumba, da kuma taron manema labarai a ranar 29 ga Satumba a babban birnin tarayya, Abuja.