A ranar Laraba ne Majalisar Dattawan Najeriya ta sanar da jingine aiki kan ƙudirin dokokin haraji na ƙasar, wanda Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya gabatar mata.
Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Barau Jibrin – wanda ya jagoranci zaman – shi ne ya sanar da hakan yayin da suke muhawara zauren majalisar.
Barau ya kuma sanar da kafa wani kwamati da zai yi aikin dubawa da kuma gyara saɗarorin dokar da ke jawo taƙaddama, musamman daga yankin arewacin ƙasar.
A makon da ya gabata ne ƙudirorin huɗu suka tsallake karatu na biyu a majalisar, daga nan kuma Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio ya miƙa wa kwamatin kuɗi domin ci gaba da aiki a kansu kafin karatu na uku kamar yadda dokar majalisa ta tanada.
Muna farin ciki shugaban ƙasa ya ji koke-koken mutane, amma da ma mu ba mu niyyar amincewa da wannan ƙudiri ba,” in ji Sanata Abdul Ningi cikin wata hira da BBC jim kaɗan bayan ɗaukar matakin.
Wasu daga cikin sanatocin kwamatin sun haɗa da Titus Zam (jihar Binuwai), da Orjir Uzor Kalu (jihar Abia), da Sani Musa (jihar Neja), da Abdullahi Yahaha (jihar Kebbi).
Hakan na zuwa ne ƙasa da kwana ɗaya bayan Shugaba Tinubu ya umarci ma’aikatar shari’a ta ƙasar ta yi aiki tare da majalisar dokokin domin samun masalaha kan wasu ɓangarori na dokar da ake taƙaddama a kai.
Tattaunawa kan ƙudurin ta janyo zazzafar muhawara a faɗin Najeriya, yayin da wasu ɓangarorin ƙasar suka yi zargin cewa an cusa wasu abubuwa da za su cutar da wasu yankunan ƙasar.