Home Labarai Duniya NDLEA ta Kama Dilar Kwayoyi a wani sumame a Kano

NDLEA ta Kama Dilar Kwayoyi a wani sumame a Kano

52
0

Hukumar Hana Sha Da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kano NDLEA ta yi nasarar kama wani dilar kwayoyi.
Hukumar ta yi nasarar cafke matashin ne a unguwar Fagge a wani sumamame da ta kai a daren Laraba.

Jami’in hulda da jama’a na hukumar a Kano, Sadiq Muhammad Maigatari ne ya bayyana hakan, yana mai cewa sun yi nasarar kama mai sayar da kwayoyin a karkashin kwamitin wanzar da zaman lafiya da inganta tarbiyyar matasa na jiharKano.

“Matashin ya fada cikin wata katuwar kwalbati mai ruwa yayin da muke kokarin kama shi a lokacin da yake kokarin tserewa”. In ji shi.

Jami’in ya yabawa kwamitin sannan ya yi kira ga alumma da su dinga bayar da hadin kai ga jami’an hukumar ta hanyar bayar da bayanan sirri kan duk wani mai hulda da miyagun kwayoyi a jihar