Shahararriyar mawaƙiyar Amurka Rihanna ta haifi ƴarta mace ta farko tare da abokin zamanta ASAP Rocky.
An sanya wa jaririyar sunan laƙabin mahaifinta – sai dai an canza harafin ƙarshe na sunan, daga ‘y’ zuwa ‘i’.
An haifi yarinyar – wadda yanzu sunanta Rocki Iris Mayer ne a ranar 13 ga watan Satumba, kamar yadda mawaƙiyar ta sanar a shafinta na Instagram, inda ta wallafa hotonta rungume da ɗiyar tata.
Dama a bikin Met Gala ne iyayen suka sanar da cewa Rihanna na ɗauke da juna biyu.
Rihanna da Asap na da ƴaƴa biyu maza Riot da RZA.
Masoya mutanen sun yi maraba da labarain haihuwar ta Rihanna, inda sanawar ta samu ‘likes’ miliyan biyar a cikin awa biyu.
Rihanna ta haifi ɗanta na farko RZA ne a 2022, sai na biyu Riot a 2023.





