Home Labarai Duniya Gwamnati ta Dakatar Da Karbar Kudin Makaratunta A Sokoto

Gwamnati ta Dakatar Da Karbar Kudin Makaratunta A Sokoto

54
0

Gwamnatin Jihar Sakoto ta dakatar da karɓar kuɗin makaranta a dukkanin makarantun sakandare mallakinta a duk fadin jihar.

Kwamishinan Ilimin Firamare da Sakandare, Farfesa Ladan Ala, ya bayyana haka, yana mai cewa dole ne dukkanin shugabannin makarantu su daina karɓar kuɗi daga hannun ɗalibai ko iyaye har sai an bayar da sabon umarni.

Farfesa Ladan ya ce, an kafa kwamiti na musamman domin duba koke-koken da ake yi kan kuɗaɗen da ake karɓa a makarantun.

“Ba a yadda a karɓi kuɗi irin su kuɗin PTA da kuɗin shiga makaranta da kuɗin takardar shaidar kammala karatu, da kuɗin MSS da fom ɗin tantancewa da kuɗin SSCE da kuma kuɗaɗen shaidar NECO/NABTEB/NBAIS ba a halin yanzu.

Mai magana da yawun ma’aikatar, Ibrahim Mohammad Iya, ya gargadi shugabannin makarantu cewa duk wanda ya saɓa wa wannan umarni zai fuskanci hukunci nan take.