Mahukunta a Amurka sun tabbatar zargin da ake yi wa tsohon daraktan hukumar tsaro FBI James Comey da yin karya ga majalisar dokokin kasar da kuma kawo cikas ga shari’a.
Shugaba Trump ya kori Comey ne a shekarar 2017, jim kadan bayan da aka tabbatar da cewa yana gudanar da bincike kan alakar kwamitin yakin neman zabensa da Rasha.
Ana tunanin tuhumar da ake wa Comey na da alaka da shaidar da ya bai wa kwamitin shari’a na majalisar dattawan kasar a shekarar 2020.
A lokacin ne ake zargin ya musanta sakin wasu bayanan sirri ga kafafen watsa labarai game da katsalandan din da ake zargin Rasha ta yi a zaben kasar na 2016.
Comey dai ya mayar da martani kan tuhumar da ake yi masa, inda yace yana maraba ya fuskanci shari’a a halin yanzu.





