Tirelar ɗauke da kaya wacce birkinta ya ƙwace ta murƙushe Keke NAPEP, inda nan take ta kashe biyu daga cikin fasinjojin.n
An samu rahoton cewa haɗarin ya afku ne da misalin ƙarfe 7 na safiyar ranar Juma’a, a kusa da rukunin gidajen ma’aikatan Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta jihar Kogi, a Lokoja, inda wata tirela ɗauke da kaya birkinta ya ƙwace ta murƙushe babur mai ƙafa uku (Keke NAPEP), inda nan take ta kashe biyu daga cikin fasinjojin.a
Katin shaidar da aka samu na ɗaya daga cikin ɗaliban mata da suka rasu yana ɗauke da sunan, Covenant Omolola Isaac, a Tsangayar Nazarin Ƙasa na Jami’ar Tarayya Lokoja.